YANDA AKE KAFI DADI
YADDA AKE YIN SARKIN DADI
YADDA AKE YIN SARKIN DADI
Kayan Hadi:
Nama
Kwai
Fulawa
Dankali
Albasa,
Attaruhu
Tumatur
Tafarnuwa
Tsinken sakace
Maggi
Gishiri
Karas
Mai
Yadda Ake Yi:
Zaki samu namanki mai kyau mara kitse ki wanke ki yanka kanana ki jajjaga attaruhu ki zuba akai sai ki zuba dakakkiyar tafarnuwa da curry kisa magi da gishiri ki dora akan wuta yayi ta dahuwa har ruwan ya kone san nan kuma ya dahu.
Ki dafa dankali ki yankashi shima a kwance da dan tudu sai ki yanka tumatur shima a slice ki yanka albasa.
Sai ki dauko dankali ki soka a jikin tsinken sakace yaje karshe sai ki saka nama shima sai ki soka tumatur sai ki kuma soka nama ki sa karas sai ki kuma saka nama sai ki aje, haka zakiyi harki gama.
Sai ki fasa kwai ki kadashi idan 4 ne sai ki zuba fulawa cokali 3 kisa magi ki juya sosai, sai ki dora mai akan wuta ki dauko wannan hadin da kika jera a hankali ki saka a cikin kwan nan ki juya ko ina ya samu sai ki soya ki barshi yayi ja har ki gama.
Created at 2020-01-01 18:00:36
Back to posts
UNDER MAINTENANCE
Welcome to my new mobile site, Barka da zuwa dan uwana shafin hausa novels sokoto,ka duba sama zaka ga an saka click here to hausa novels kusa da inda aka saka About me to ka danna rubutun kawai ko ka shiga wurin zaka samu sabbin litattafai
"Trouble shared is trouble halved."