
Maganin kansa na a cikin tururuwa
Masanan kasar Rasha sun gano wani sabon sinadari a hanjin tururuwa wanda ka iya magance wasu nau'o'in cutar daji,wato Cancer.
Masanan kasar Rasha sun gano wani sabon sinadari a hanjin tururuwa wanda ka iya magance wasu nau'o'in cutar daji,wato Cancer.
Masanan na Rasha wadanda kwararru ne a fannin ilimin kiwon lafiya sun gano wata kalar kwayar halitta (Bacteria) a cikin hanjin wata tururuwa wacce aka fi sani da "Camponotus Vagus" a duniyar masana.
An sanar da cewa kwayar halittar na sarrafa wani sinadari mai wuyar samu "Nybomycine" wanda ka iya warkar da wasu nau'o'i na cutar daji.
Wannan wani babban albishir ne,musamman a wadannan 'yan shekarun,inda aka gano cewa akwai kwayoyin halitta na cutar kansa da dama da suka gagari magani.Abin da masana suka dukufa neman wasu sabbin hanyoyin da magance cutar.
Masanan Rasha sun fi maida hankali kan tururuwa wacce ke iya rayuwa ko a cikin matsanancin yanayi na kiwon lafiya.Manufarsu ita ce, gano yadda wadannan kwarin ke kare kansu da kwayoyin halittun da ke kewaye da su
UNDER MAINTENANCE