YANDA AKE ALKAKI
ALKAKI
INGREDIENTS:
1. Alkama mudu ďaya
2. Sugar gwangwani 6
3. Nono na shanu
4. Man shanu ďanye
5. Butter simas rabi
6. Mai kwalba biyu
A sheqe alkama a cire dukkan dattin ko a wanke
a baza shi a rana ya bushe. Sai a kai babban inji
a mishi 'barjin fate idan aka dawo dashi a bude
tsakiyar alkaman a kwanon kwabi a juye nonon
shanu, butter, man shanu, sai a murje shi da
kyau ya hade. Sai a zuba ruwa amma kwabi zaki
mishi mai qarfin gaske yanda zai hade da kyar,
Sai a rufe shi ya kwana.
Idan kika tashi da safe sai ki jiqa kanwa, ki rinqa
yayyafa masa kina hadashi kina bugawa. Har sai
kin diba a hannun ki kin masa naďin alkaki kin ga
bai karye ba. Wato kin yi tsaho dashi kin murza
duka bai karye ba. Kin ga ba qaramin bugu zaki
masa ba. Ba a jibga masa ruwa sam, yayyafa
masa zaki rinqa yi kina buga shi.
Sai a zuba sugar a tukunya, a zuba ruwa kamar
kofi uku a ďaura a wuta. Idan mai buqatar sugar
alkakin ya rinqa ďiga ne bayan ya gama shiga
cikin sa sai ki saka tsamiya kwaya đaya ko table
spoon na lemun tsami yayin da kike dafawa. In
kuma kina son ya bushe a jikin sa kamar nawa to
kada kisa.
Wurin dafa sugar a kula yana fara yin kumfar
farko na dahuwa a ďiba a cokali yana ďan fara
shan iska zaki ga yayi danqo. Sai a sauke don
haka kada ki barshi yayi ta dahuwa kamar na
tuwon madara ko aya.
Sannan wurin soya alkakin a saka mai aqalla
kwalba biyu ko fiye, baya shan mai sam amma
yana buqatar mai wurin soya shi. Kuma wutan
kadan-kadan yanda cikin zai soyu. Bayan kin
tsane shi a mai straight a cikin sugar zaki saka,
idan kina gabda tsamewa sai ki kwashe na cikin
sugar ki sa a kwanon da zaki ajiye.
Note: Idan kin yi wanda baki so sugar yana bin
sa ne zai ďan rinqa daskarewa sai kina yi kina
ďan narkar dashi. Sannan ludayin da zaki rinqa
amfani dashi wurin suya daban, na sakawa a
sugar shima daban. Masu tambaya akan abun da
basu gane ba zasu iya yi. Wainda basu iya yin
naďin shi ba su nemi wainda suka iya su koya
musu. Zaku ga wasu alkakin su yayi ja wasu sun
yi haske yanayin alkaman ne amma babu
damuwa.
Created at 2020-01-01 21:34:08
Back to posts
UNDER MAINTENANCE
Welcome to my new mobile site, Barka da zuwa dan uwana shafin hausa novels sokoto,ka duba sama zaka ga an saka click here to hausa novels kusa da inda aka saka About me to ka danna rubutun kawai ko ka shiga wurin zaka samu sabbin litattafai
"If you can't stand the heat, get out of the kitchen."