
YADDA AKE YIN SPICY LIVER
YADDA AKE YIN SPICY LIVER
Kayan Hadi:
Hanta
Kwai 5
Tafarnuwa 1
Albasa 1
Curry
Man gyada
Maggi
Attaruhu 5
Leda
Yadda Ake Yi:
Zaki gyara hantarki ki wanketa ki markadata a blander ki juyeta a kwano ki ajeta, ki markada attaruhu da tafarnuwa idan kina so ki tsiyaye ruwan a ciki banda cito citon sai ki zuba maggi curry da dan gishiri a ciki sai ki jujjuya ki zuzzuba aleda kamar alala ki dafashi kamar yadda kike dafa alalan leda,
Idan ya dahu zakiga ya hade jikinsa saiki sauke ki kwance ledar ki yi masa irin yankan da kike so, sai ki fasa kwai ki kadashi kisaka maggi sannan ki dora mai akan wuta ki dinga dauka kina tsomawa a kwai kina soyawa har ki gama zaki iyayin sa da safe ki sha da kunun shinkafa.
UNDER MAINTENANCE