
Shan taba sigari na daga cikin matsalolin da suka fi lashe rayukan mashaya tabar. Kuma duk cikin mashaya taba biyu, ɗaya daga cikinsu kan mutu ne sakamakon cutukan da shan tabar ke jefa su.
Shan taba sigari na da gagarumar illa ga dukkan sassan jiki kamar haka:
1. Zagayawar jini: Kamar yadda aka sani ne cewa; zagayawar jini shi ne ci gaban rayuwa. Sai dai, yayin da gubar da ke ɗauke cikin hayakin taba sigari ta shiga cikin jini hakan zai sa:
i. Kaurin jini ya qaru, wannan zai ƙara haɗarin daskarewar jini a cikin jijiyoyin jini.
ii. karuwar hauhawar jini da ingiza bugawar zuciya fiye da kima; wannan zai kara wa zuciya wahalar harba jini zuwa sassan jiki.
iii. Cushewar ko matsewar jijiyoyin jini; wannan zai rage wa sassan jiki samun isashshen jini da iskar oksijin.
2. Lahanta huhu: Huhu wanda nan ne sashin da ake canjin iska tsakanin iskar oksijin (oxygen) da muke shaƙa da kuma iskar kabon (carbondioxide) da muke fitarwa. Shan taba sigari na rage wannan aiki na canjin iska, baya ga lalata tanadin kariya da Allah ya shirya wa huhun, wannan zai karya garkuwar huhun ta yadda cutukan numfashi kamar tarin fuka (TB), kumburin kwaroron huhu, daji / kansar huhu za su kama mutum cikin sauki.
Waɗannan illoli na shafar dukkan sauran sassan jiki kamar zuciya, jijiyoyin jini, kayan ciki, fata, kashi da raguwar kwayoyin halittar haihuwa da dai sauransu.
3. Jinkirin warkewar karaya: Muggan sinadaren da suke cikin hayakin taba na hana kwayoyin halittar kashi hayayyafa ko tsatstsafowa da wuri bayan karayar kashi domin samun haɗewar gurbin karayar.
Wannan ya sa masu shan taba sigari ke samun karin tsawaitar lokacin da karaya ya kamata ta warke, ko kuma rashin haɗewar kashin ma ɗungurungum.
4. Lahani ga ido: Taba sigari na lahanta ido kamar yadda take lahanta huhu.
i. Duk da alakar da ke akwai tsakanin shan taba sigari da makanta, mutum ɗaya cikin biyar ne kawai ke da masaniya kan hakan.
ii. Mashaya taba na da ninki biyu na haɗarin rasa ganinsu fiye da waɗanda ba sa sha.
iii. Hayakin taba na ɗauke da muggan sinadaran da ke tunzira ko lahanta ido.
iv. Misali, muggan ɓirɓishin karafe nau'in "lead" da "copper" na iya taruwa a gilashin ido (eye lens) su kuma kawo larurar dindimin ido.
v. Shan taba sigari na ta'azzara ciwon idon da ciwon siga ke kawowa ta hanyar toshe jijiyoyin jinin ido.
vi. Kuma mashayan taba na da ninki goma sha shida fiye da marasa sha na haɗarin makanta sakamakon toshewar jijiyoyin jinin ido.
vii. Shan taba na da haɗarin ta'azzara ko janyo matsalolin gani wanda ya zama wajibi mashayan su kaurace mata.
A takaice dai, bayan duk ɗinbum illolin shan taba sigari, duk wata cuta ko larura shan taba sigari na da tasirin ta'azzara ta.
UNDER MAINTENANCE