
1. Hanta guda ce daga cikin muhimman kayan ciki. Kuma tana nan a cikin ciki a ɓangaren dama daga sama, kasa da faffaɗar tsokar nan da ta shingice tsakanin ciki da ƙirji.
2. Nauyin hantar mutum ya kai nauyin kilogiram ɗaya da rabi (1.5kg).
3. Hanta na samun jini da ya kai yawan lita ɗaya da rabi a kowane minti (1.5L).
4. A hanta ne ake gama narka sinadaran abinci yadda jiki zai iya amfani da su kamar dangogin siga, furotin, kitse, nau'o'in, magani, bitamin da sauransu.
5. Hanta taska ce da ke ajiye muhimman sinadarai zuwa lokacin da jiki zai buƙace su, kamar siga, narkakken furotin, nau'o'in bitamin da sauransu.
6. Hanta na samar da sinadarai kamar gulokos, narkakken furotin da sauran muhimman sinadaran da jiki ke buƙata.
7. Hanta ce ke samar da ruwan maɗaciya. Ruwan maɗaciya na amfani wajen narka kitse yadda jiki zai iya zuƙar sa daga hanji zuwa cikin jini.
8. Hanta na yin aikin kawar da guba, muggan sinadarai da kwayoyin cuta kamar bakteriya da bairos.
9. Hanta na sarrafa / samar da jini ga ɗan tayi, haka nan, tana ajiyewa da samar da muhimman kayayyakin sarrafa jini kamar sinadaran 'vitamin B12' da 'Iron'.
10. Jajayen kwayoyin jini na shafe kwanaki 120 suna rayuwa ne. Hanta na kashe raunanan jajayen kwayoyin jini bayan sun cika kwanaki 120 suna aiki.
11. Hanta ce sashin da ke samar da mafi yawan zafi / ɗumi da jiki ke amfani da shi wajen ci gaban rayuwa.
12. Hanta ɓangare ne na garkuwar jiki. Domin hanta na samar da sinadaran da ke yi wa garkuwar jiki kaimi, bayan nan, tana yaƙar bakin abubuwa da ke shiga jiki ta hanyar abinci, harbin kwayoyin cutuka da sauransu.
UNDER MAINTENANCE