Dalilai da yawa sun nuna mana cewa matan sauran kabilu sun fi na Malam Bahaushe dadin zama, hakan ta sa a yau, za mu tattauna akan wasu dalilai da ke sa matar Bahaushe rashin more dadin zaman aure kamar haka:
*1.Raini: Akwai tsabar raini ga matar malam bahaushe,zaku zauna da mace shekara da shekaru amma rana daya matsala ta samu za ka ji maganganu na raini ka ji suna cewa mazajensu kaddara ce ta sa suka aure su. Sai ka ji suna cewa ‘Idan ba kaddara ba, ba abunda zaisa na aureka, Ai namiji ba dan goyo da zani ne ba,d aman duk wacce ta dauki namiji uba za ta mutu marainiya da dai sauran kalamai irin wadannan
In muka yi wa wadannan kalamai fassara na tsanaki, za mu fahimci abinda matar Bahaushe ke nufi da su. Za mu gane manufarta ita ce kada mace ta sake ta baiwa mijinta yadda dari bisa dari, kada ta bashi soyayyarta duka. wanda kuma daga nan ne matsalar auratayya ke farawa
Hakan tasa mazan hausawa da yawansu, suna zaune da matan sune bisa lalura kawai, saboda abin haushi da kularwa da matan ke nuna musu wai da sunan kar su nunawa mazan soyayya da yarda wai don hakan zai iya cutar da su. KUMA ABIN MAMAKI DA YAWAN MATAN HAUSAWA SUNA DA WANNAN RA’AYIN, sabanin sauran kabilu za ka samesu basa raina mazajensu
*2.Rashin yi wa miji hidima: A nan ma za ka ga sauran matan kabilu suna yi wa mazajensu wanki da guga da wanke takalmi da lura da kwalliyar maigida da gyara masa ado, wasu har gona suke zuwa, daukar nauyin karatun ‘ya’ya da sauransu.. amma matan bahaushe babu ruwansu, sai dai su ci su kwanta, babu ruwansu da mijinsu, balantana su yi masa wata hidima.
Hidimar kawai da za ta yi masa shi ne, ta dafa masa abinci, ko ta kai masa ruwan wanka. BA WAI AN CE A ADDINANCE WAJIBI NE SAI TA YI HIDIMA KAMAR BAIWA BA, A’A, AMMA TA FUSKAR MALLAKE MIJI DA NUNA MASA KAUNA SAI KIN YI MASA HIDIMA DAI DAI DA ARZIKINSA ,MISALI GYARA MASA KWALLIYA, GOGE MASA TAKALMI DA JAKA, DAURA MASA BELIT KO MADAURI WUYA, GYARA MASA FUSKA DA KILIFA, GYARA MASA HULA, RIKE MASA JAKA, IN ZAKI IYA YI MASA WANKI MA TO BA LAIFI, AMMA BA TILAS.
Wadansu matan kabilun ma har yi wa mazansu sutura suke yi tare da yi musu kyaututtukan bazata. Duk wannan yana kara soyayya da shakuwa tsakanin ma’aurata
A nan ba ina nufin namiji ya kwanta kawai matarsa ta rika yi masa hidima da baut aba kamar yadda ake yi a wasu guraren kaga an maida mata tamkar bayi suyi casa suyi surfe suyi niqa,da shauran aikin wahala hakan bai dace ba dan bautar da mata laifi ne a addininmu . AMMA KODA MIJINKI MAI KUDI NE, TO YANA BUKATAR HIDIMA KODA DA KYAUTATAWACE
3*Rashin godiya: Matar bahaushe tana da wata al’ada ta rashin godewa kokarin da mazajensu suke yi musu. Ba su nuna godiyar a aikace ko kuma su furta da baka. Akwai matan da suke cewa mazajensu mai suka taba yi musu tun da na zo hanunka WANNAN KALMA CE MAI MUNI. Daruruwan shekarun da suka gabata ANNABI S.A.W ya suffanta mata masu irin wannan dabi’a, amma abin mamakin shi ne yadda kasan da matan Hausawa Annabi S.A.W ya ke don bincike ya nuna sun fi sauran mata fadarta.
Akwai nau’o’i na nunawa miji godiya, kuma WALLAHI DUK SADDA KI KA NUNAWA MIJI GODIYA SAI YAJI YA KARA SONKI. KIN GA ASHE RIBARKI CE MA.
Amma abin haushi ‘yan kalmomi kadan da za ta furtawa mijinta hade da murmushi da kyakkyawan kallo shikenan fa, kin farantawa mijinki rai kin kara samun matsayi a zuciyarsa, ga kuma hidimar da ya yi miki ga addu’ar da mala’iku za su yi miki
Sau tari, in Kaga matar Malam bahaushe tana yi wa mijinta godiya da fara’a to ta cuce shi ne ko kuma tana shirin cutarsa
*4 boye soyayya ga miji: ita ma wata dabi’a ce ta matan hausawa ,rashin nunawa miji soyayya sai dai baya-baya, dan wasu matan sun dauka nunawa miji soyayya nasa miji ya rainaki. Wannan ma sai ya sa kaga ba a yi masa komai. SU MATAN HAUSAWA ABINDA SUKA DAUKA NUNA SOYAYYA GA MIJI ITA CE KAWAI KWANCIYAR AURE, bayan haka ba wata soyayya da suke nunawa mazajensu, sau tari za ka ji matan wasu kabilun suna cewa “Wallahi da za su hada kishi da bahaushiya sai sun kwace mijin, ba malamai ba boka kawai tsantsar nunawa miji kulawa da soyayya da hidima.
*5 Watsar da kwalliya bayan aure da rashin iya tsara kwalliya:
Matar malam bahaushe da zarar ta yi aure bayan ta gama cinye amarcinta hakanan za kaga tawatsar da dabi’arta ta kwalliya ta koma daura zani iya kirji, kwaskwarima, bare tafara tara ‘ya’ya, Subhanallah! Hakanan suke har wajen tsarin sanya sutura, ba sa tsayawa su fahimci wace iriyar sutura ke burge mazajensu don rike irin wannan sutura a matsayin suturar da za su sanya a kebantaccen lokacinsu tare da mazajensu. Wata sai kaga tana ta daura atamfa alhali siket da ‘yar riga ke burge mijinta
*6:RASHIN IYA KISHI:
matar bahaushe ba ta iya kishi ba, KISHI ANA YIN SA NE DON A MALLAKE MIJI TA HANYAR KYAUTATA MASA, AMMA ITA MATAR BAHAUSHE SAI DAI A BATAWA MIJI RAI.
Afuwa gareku matan Hausawa wannan bayani badan ya yi muku zafi na yi shi ba, a’a, illa kawai, don na tunatar da ku irin halayen mafiya yawanku matanmu na Hausawa. An yi muku nisa a fagen zamantakewa kamar yadda ku ka sani, yau duniya ta ci gaba sosai a kowanne bangare, wannan kuwa ya hada har da bangaren zamantakewa. A saboda haka ne ma na ke yin kira a gareku da ku canja. Admin Abdul
UNDER MAINTENANCE