*Yadda Ake hada abun kyautata kamshin iska (air freshner)*
07068808039
Yan uwa muna maku maraba da sake kasancewa a tare daku cikin wannam gida mai Albarka na hausanovels.
To a yau ma inshaallah mun taho da wata tsaraba mai girma wadda itace yadda ake hada abun kyautata kamshin iska a hausance ko mu ce air freshner a takaice to kamar yadda muka saba har kullum muna fara lissafa kayan hadin wato kayan da zaa sawo a kasuwa sannan mu je ga yadda ake hada abubuwan kabkidaya.
Shima wannan abun kyautata kamshin iska(air freshner) ana bukatar sinadarai kamar haka, amma fa a kula nan a awon mu ne ya danganta ga yadda mutum yake son yayi.
*Sinadaran hada air freshner a lissafe*
1. Turare => ana bukatar kwalba hudu (4) mai kamshin dadi ko wane irine.
2. Isanol => shikuma ana bukatar awo biyar (5).
3. Mensol => shima ana bukatar kulli daya (1) shine karfin kamshi.
4. Antisol => shi ana bukatar awo daya (1).
5. Farin sikina => ana bukatar awo (3) ne.
6. Ruwa => kashi 100.
*YADDA AKE HADAWA*
Da farko dai zaa narka Antisol da ruwa, sannan sai a zuba mensol a cikin turare ya narke, daga nan zaa zuba isanol a cikin wurin da zaa yi hadin kayan, sannan kuma sai a zuba wato shi mensol din da aka narke a cikin turaren sai a motsa su sosai har sai sun motsu sosai har kamar tsawon akalla minti goma (10), sannan sai a zuba shi a hankali a narkaken antisol din, kana motsawa, sa farin sikina, sa farin sikina da yan ruwa, sa su a cikin wurin hadin motsa su, sai a kara ruwa , ana sawa ana motsawa, tsawon minti goma, daga nan kuma sai a zuba a cikin abinda zaa kai kasuwa wato kwallabe shkenan.
ALHAMDULILLAH AN KAMMALA HADI GA MAI BUKATAR KARIN BAYANI SAI YA BIYO MU TA SHAFIN MU NA YANAR GIZO
Hausanovels.hexat.con
*_Admin Abdul_*
UNDER MAINTENANCE